Ba Wanda Za Mu Baiwa Hakuri Don Mun Gayyato Malami Daga Kasar Waje----Sarkin Musulmi
Join our subscribers list to get the latest news, updates and special offers directly in your inbox
Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar, ya ce Musulman Najeriya na da ’yancin gayyatar dan uwansu daga ko ina a fadin duniya domin ya yi wa’azi a kasar.
Basaraken na mayar da martani ne ga masu sukar lamirinsa kan gayyato fitaccen malamin addinin Musuluncin nan mai wa’azi dan asalin kasar Indiya, Sheikh Zakir Naik.
Malamin ya isa Sakkwato ne a farkon makon nan domin yi wa’azi a wasu Jihohin Najeriya, bisa gayyatar Sarkin Musulmin.
To sai dai da yake mayar da martani ga masu sukar lamirin nasa yayin rufe taron Makon Usmanu Danfodiyo da ya gudana a Sakkwato, Sarkin ya ce, “Shi Musulunci daya ne duk inda ka je.
“A matsayinmu na Musulmai, muna da damar gayyatar ’yan uwanmu Musulmai domin yin mu’amala da su. Na fara haduwa da Dokta Zakir Naik tun shekaru 11 da suka gabata.
“Sakkwato na farin cikin karbar bakuncinka. Mu muna alfahari da kasancewarmu Musulmai, kuma muna aiki ne domin ci gaban Musulunci, ba wai kowa ba.
“Mu Musulmai ne saboda haka Allah Ya ga dama, kuma babu wanda ya isa ya canza haka, muna gode wa Allah da ya yi mu a matsayin Musulmai,” kamar yadda ya bayyana yayin gangamin rufe taron a Cibiyar Taro ta Kasa da Kasa da ke Sakkwato.
Sarkin Musulmin ya ce malamin ya yi kokari matuka wajen ilimantar da Musulmai da ma wadanda ba Musulmai ba abin da Musulunci ya kunsa.Za
managarciya Feb 3, 2025 3 125
managarciya Oct 30, 2021 12 113
Maryamah Dec 16, 2021 10 90
Maryamah Dec 14, 2021 2 84
managarciya Jun 24, 2023 5 67
managarciya Nov 13, 2023 0 554
managarciya Nov 12, 2023 0 352
managarciya Nov 12, 2023 0 340
managarciya Nov 12, 2023 0 419
managarciya Nov 11, 2023 1 707
managarciya Dec 8, 2025 0 32
managarciya Apr 27, 2024 0 254
managarciya Jan 2, 2022 1 555
Sannan gwamnati da ƙungiyoyi ma su zaman-kan-su da ma ɗaiɗaikun mutane ya kamata...