BUA Ya Gina Asibiti, Makaranta Da Masallaci Na Naira Miliyan 275 A Sakkwato
Join our subscribers list to get the latest news, updates and special offers directly in your inbox
A Laraba data gabata ne kamfanin siminti na BUA ya mikawa al’ummar Gidan Boka da ke Ƙaramar Hukumar Wamakko a jihar Sakkwato wani asibiti da makaranta da masallaci, da kudinsu ya kai Naira miliyan 275.
Kamfanin ya damƙa gine-ginen, wanda tuni aka kammala, har da tagomashin ton 170 na siminti ga al’ummomi 68 a karamar hukumar.
Manajan Daraktan Kamfanin Simintin na BUA, Yusuf Binji, ya ce wannan karamcin wani bangare ne na alhakin yi wa al’ummar da kamfanin ya ke alheri.
Banji, wanda Daraktan Ma’aikata na BUA, Altine Wali ya wakilta, ya ce kamfanin ya gudanar da aikin samar da matsugunan ne a wani bangare na shirin fadada katafaren gini, tare da share filaye a cikin al’ummar Gidan Boka da kuma raba filaye ga iyalan da abin ya shafa.
Da yake jawabi, shugaban gudanarwa da ayyuka na kamfanin, Sada Suleiman, ya ce kamfanin ya kuma gina tituna, da kuma samar da makabarta, ruwan bututu da wutar lantarki ga al’umma.
Ya ce, kamfanin ya tabbatar da shirin raba siminti ga al’umma domin gyara masallatai da sauran ababen more rayuwa, da kuma samar da magunguna da sauran kayayyakin masarufi ga ‘yan kasa a cikin al’ummomin yankin.
“Kamfanin Simintin BUA yana tallafawa al’ummomin a fannin kiwon lafiya, horar da basira, samar da guraben karatu da kayan ilimi,” in ji shi.
managarciya Feb 3, 2025 3 135
managarciya Oct 30, 2021 12 127
Maryamah Dec 16, 2021 10 93
Maryamah Dec 14, 2021 2 87
managarciya Jun 24, 2023 5 71
managarciya Nov 13, 2023 0 554
managarciya Nov 12, 2023 0 352
managarciya Nov 12, 2023 0 340
managarciya Nov 12, 2023 0 419
managarciya Nov 11, 2023 1 707
managarciya Mar 3, 2024 0 300
managarciya Sep 12, 2025 0 66
managarciya Jan 1, 2025 0 208