Kotun ƙoli ta tabbatar da ikon shugaban ƙasa na ayyana dokar ta-ɓaci a kowacce jiha
Kotun Koli ta Najeriya ta tabbatar da ikon Shugaban Ƙasa a ƙarƙashin kundin tsarin mulki na ayyana dokar ta-ɓaci a kowace jiha da ke fuskantar tabarbarewar tsaro ko barazanar fadawa cikin rikice-rikice.
Hukuncin, wanda aka yanke da rinjayen Alkalai 6–1, ya biyo bayan ƙarar da Jihar Adamawa da wasu jihohi 10 da PDP ke mulki suka shigar.
Masu ƙarar sun kalubalanci ayyana dokar ta-ɓaci da Shugaba Bola Tinubu ya yi a Jihar Rivers, wadda ta haɗa da dakatar da zaɓaɓɓun jami’an jihar na tsawon watanni shida.
A hukuncinta, kotun koli ta yi watsi da ƙarar bayan ta amince da ƙorafe-ƙorafen farko kan rashin hurumin shari’a. Sai dai duk da haka, kotun ta ci gaba da duba muhimman batutuwan shari’ar, inda daga bisani ta yanke hukunci a goyon bayan matakan da bangaren zartarwa ya ɗauka.
A cikin hukuncin rinjaye da Mai Shari’a Mohammed Idris ya karanta, kotun ta bayyana cewa Sashe na 305 na Kundin Tsarin Mulki na 1999 ya bai wa Shugaban Ƙasa ikon ɗaukar “matakai na musamman” domin dawo da zaman lafiya da doka a lokacin dokar ta-ɓaci.
Kotun ta ƙara da cewa ko da yake kundin tsarin mulkin bai fayyace irin waɗannan matakai ba, sashe na 305 yana bai wa Shugaban Ƙasa damar ɗaukar matakan da suka dace, ciki har da dakatar da zaɓaɓɓun jami’ai na ɗan lokaci, muddin an kayyade tsawon lokacin matakan kuma an yi su ne domin dawo da daidaito da zaman lafiya.
A ra’ayinsa na ƙin amincewa da hukuncin , Mai Shari’a Obande Ogbuinya ya ce duk da cewa Shugaban Ƙasa na da ikon ayyana dokar ta-ɓaci, wannan iko bai kai ga dakatar da zaɓaɓɓun jami’an da aka zaba bisa dimokiraɗiyya ba, ciki har da gwamnonin jihohi, mataimakan gwamnonin jihohi, da ‘yan majalisun dokoki na jihohi.
managarciya