NAFDAC ta kwace Katon 24 na Magi Dunkule da ya lalace a Sokoto
Join our subscribers list to get the latest news, updates and special offers directly in your inbox
A cewarsa masu sayarda kayan in aka kama su sai su rika fadin ba su San kayan abincin sun lalace ba domin ba su duba kwanan watan kayan balle su san wa'adin da aka diba na amfani da su ba, a hakan za su shigo da kayan abinci da ya gurbata ko yake kusa da lalacewa a rika sayarwa mutane a shaguna da kasuwa.
Garba Adamu ya ce wanda hukumar ta kama za a hukunta shi, bayan karbe Magin da aka yi domin ya zama guba bai kamata mutane su yi amfani da su ba.
Ya yi kira ga mutanen Nijeriya a koyaushe su rika duba rijistar NAFDAC da Kuma kwanan watan da Kamfani ya dibarma kayan a yi amfani da su kafin su saye ko su yi amfani da su.
Adamu ya godewa jami'an tsaron da ke taimakawa hukumar da kungiyoyin 'yan kasuwa na jiha da daidaikun mutane da kungiyoyin cigaba da ke taimakawa NAFDAC domin tsare lafiyar al'umma.
"Wasu 'yan kasuwa nada halin kawo kayan da suka gurbace ko suka yi kusan lalacewa a kasuwar Sakkwato da wajenta, wasu Kuma a tafi da su a kasuwannin Boda da kauyukka domin a sayar da su," a cewarsa.
Kodineta ya gargadi masu sayarda kayan da suka gurbata ko suka lalace da wadanda ba su da rijistar NAFDAC masu yin haka doka za ta yi aikinta kansu a kowane lokaci aka samu nasarar damke su.
managarciya Feb 3, 2025 3 126
managarciya Oct 30, 2021 12 110
Maryamah Dec 16, 2021 10 92
Maryamah Dec 14, 2021 2 86
managarciya Jun 24, 2023 5 69
managarciya Nov 13, 2023 0 554
managarciya Nov 12, 2023 0 352
managarciya Nov 12, 2023 0 340
managarciya Nov 12, 2023 0 419
managarciya Nov 11, 2023 1 707
managarciya Oct 10, 2021 0 299
“A matsayina na ‘yar jihar Sakkwato ina jin takaicin zaman banza da lalaci da maula,...
managarciya Sep 18, 2024 0 358
managarciya Jan 1, 2024 0 300
Wasu mutane na ganin tun farko gwamnti ta yi ragon azanci don bai kamata ta sayi...
managarciya May 9, 2022 0 559
managarciya May 12, 2023 0 249
managarciya Sep 16, 2025 0 43
managarciya Dec 10, 2025 0 61
managarciya Nov 24, 2021 0 423
Sanin kowa ne kudade sun yi ƙaranci a hannun jama'a, kuma gashi muna bukatar abinci...