Bayan umarnin Gwamna Abba, Ganduje ya janye shirin kafa Hisbah mai zaman kanta a Kano
Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya janye shirin da ya yi na kafa wata Hisbah mai zaman kanta da ake kira Hisbah Fisabilillahi a Jihar Kano.
An bayyana wannan mataki ne cikin wata sanarwa da wani jigo a jam’iyyar APC a Kano, Dr. Baffa Babba Dan Agundi, ya fitar tare da sanya wa hannu.
A cewar sanarwar, matakin ya biyo bayan taron masu ruwa da tsaki da ya haɗa wakilai daga ƙananan hukumomi 44 na Jihar Kano. An gudanar da taron ne a Ofishin Kamfen na Tinubu.
Sanarwar ta bayyana cewa an yanke shawarar janyewa daga shirin ne bayan martanin jama’a da damuwar da aka nuna dangane da shirin kafa Hisbah mai zaman kanta.
DAILY NIGERIAN HAUSA ta rawaito Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf na bada umarnin dakatar da shirin kafa Hisbar inda ya umarci jami'an tsaro su dau mataki kan masu shirin.
managarciya