Jiragen yaƙi Guda 24 da Najeriya ta siya a Italiya na dab da isowa ƙasar nan
Najeriya na shirin karɓar jiragen yaƙi M-346 guda 24 daga ƙasar Italiya, a matsayin mafi girman sayen jiragen soji da aka taɓa yi a Afirka ta Yamma.
Rundunar Sojin Sama ta Najeriya ta kulla yarjejeniya da kamfanin tsaro na Italiya, Leonardo, a watan Nuwamba 2023, wadda rahotanni suka ce ta kai kimanin euro biliyan 1.2.
Yarjejeniyar ta kuma haɗa da tallafin kayan aiki da gyara na tsawon shekaru 25.
Ana sa ran jirage shida na farko suna kan aikin kera su a Italiya, inda za a kawo uku a shekarar 2025, yayin da ake sa ran kammala kawo duka jiragen zuwa tsakiyar 2026.
Babban Hafsan Sojin Sama a lokacin sayen jiragen, Hasan Abubakar, ya ce jiragen za su ƙarfafa horaswa da kuma inganta ayyukan soji, musamman wajen yaƙi da Boko Haram, IS, da kuma fuskantar matsalolin tsaro kamar garkuwa da mutane da fashin daji a ƙasar.
managarciya