INEC ta gana da bangarori biyu na PDP dake ikirarin shugabancin jam'iyyar 

INEC ta gana da bangarori biyu na PDP dake ikirarin shugabancin jam'iyyar 

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta gana da ɓangarori biyu na jam’iyyar PDP a hedikwatarta da ke Abuja.

Taron na da nufin warware rikicin shugabanci da ya daɗe yana addabar jam’iyyar PDP.

Shugaban Hukumar, Farfesa Joash Amupitan, ya ce INEC na da alhakin, bisa ga kundin aikinta, ta shiga tsakani wajen warware matsalolin da ke cikin jam’iyyun siyasa, musamman gabanin zaɓen kananan hukumomin Abuja, da kuma zaɓukan gwamna na Ekiti da Osun da za a gudanar.

A cikin tawagar kwamitin gudanarwa na ƙasa  da Kabiru Turaki ke jagoranta akwai Shugaban Kwamitin Amintattu, Sanata Adolphus Wabara, tsohon Gwamnan Jihar Neja, Dakta Mu’azu Babangida Aliyu, da sauran manyan jiga-jigan jam’iyyar.

Shi ma kwamitin gudanarwa na ƙasa  da Abdulrahman Mohammed ke jagoranta yana tare da Sanata Samuel Anyanwu, Kyaftin Umar Bature, da wasu da dama.