Zargin Ɗangote ga Faruk Ahmad: Za a gudanar da cikakken bincike kan shugaban NMDPRA -  in ji ICPC

Zargin Ɗangote ga Faruk Ahmad: Za a gudanar da cikakken bincike kan shugaban NMDPRA -  in ji ICPC

Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa da Sauran Laifuka Masu Alaka da Su (ICPC) ta tabbatar da karɓar ƙorafi daga attajirin ɗan kasuwa, Alhaji Aliko Dangote, kan Shugaban Hukumar Kula da Harkokin Man Fetur ta Kasa  (NMDPRA), Farouk Ahmed.

A ranar Lahadi, Dangote ya zargi Ahmed da kashe dala miliyan biyar ($5m) a matsayin kuɗin karatun ’ya’yansa a makarantu da ke ƙasar Switzerland.

Attajirin ya kuma zargi shugaban NMDPRA da yi wa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa, tare da miƙa ƙorafi ga ICPC bisa zargin cin hanci da rashawa.

Da take martani ga ƙorafin, ICPC a ranar Talata ta ce za ta binciki lamarin.

“ Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa da Sauran Laifuka Masu Alaka da Su (ICPC) na sanar da cewa ta karɓi ƙorafi a hukumance a yau Talata, 16 ga Disamba, 2025, daga Alhaji Aliko Dangote ta hannun lauyansa. Ƙorafin ya shafi Shugaban NMDPRA, Alhaji Farouk Ahmed.

“ICPC na so ta bayyana cewa za a binciki ƙorafin yadda ya kamata,” in ji sanarwar da kakakin ICPC, John Odey, ya fitar.